Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC ta cafke wani mutum mai suna Mustapha Muhammad, wanda aka fi sani da Mustapha Naira bisa zargin yada jita-jita a fannin harkokin kudi a kasar.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da hukumar ta ranar talata, wanda hukumar ta bayyana cewa ta kama shi ne ranar 12 ga watan nuwamba a yankin wuse zone B wadda ke matsayin cibiyar hada-hadar kasuwancin chanjin kudi a birnin tarayya Abuja.
Read Also:
Hukumar tace kame na guda cikin ayyukan da ta ke yin a tsaftace harkokin chanjin kudaden waje da kuma kawar da dukka masu kawo tasgaro a fannin da kuma yin zagon kasa ga tattalin arzikin kasar.
“wanda ake zargin yayi wasu bayanai masu amfani a daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da bincike” a cewar EFCC.
Idan dai za’a iya tunawa hukumar EFCC ta kai sumame kasuwannin chanjin kudi, dake Nijeriya da suka hadar da jihohin legas, kano dama birnin tarayya kasar Abuja, wani bangare na dakatar da sauyin kudin kasar da Dalar Amurka abinda ake kallon ya kara sanya farashin dalar tashin gwauron zabi.
An zargi yadda wasu ke halasta kudin haram ta hanyar sauya su da dala, da nufin kada su yi asarar su sakamakon sake fasalin kudin kasar da Gwamnati tayi Shirin yi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 23 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 4 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com