INEC za ta Tattauna da Ganduje, Bala Muhammad, da Jami’an Tsaro Kan Batutuwan Zaben 2023

Hukumar zabe mai zaman kanta za ta tattauna da jiga-jigan siyasar kasar nan kan batutuwan da suka shafi zaben 2023.

An gayyaci wasu gwamnoni, dan takarar shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki na kasar nan.

Majiya ta bayyana maudu’in da za a tattauna a kai don shawo kalubalen tsaro a zaben 2023 mai zuwa na badi.

FCT, Abuja – Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a ranar Talata mai zuwa za ta gana da gwamnoni, jami’an tsaro da dan takarar shugaban kasa gabanin zaben 2023 mai zuwa nan kusa.

Za a yi tattaunawar ne a Nicon Luxury a birnin tarayya Abuja tare da kwamishinan INEC kan harkokin wayar da masu kada kuri’u, Festu Okoye, Punch ta ruwaito.

A bangaren ‘yan siyasa, za a zauna da gwamna Abdullahi Ganduje na Kano, gwamna Bala Muhammad na Bauchi da gwamna Samuel Ortom na jhar Benue.

A bangaren hukumomin tsaro, za a yi zaman tare da sufeta janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba da dai sauransu.

Hakazalika, za a yi da dan takarar shugaban kas ana jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, shugaban majalisar zauren shawarin jam’iyyun siyasa, Yabagi Sani, kungiyar ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki a harkar zabe.

Wannan batu dai na fitowa ne a cikin wata sanarwa da wanda ya shirya zaman, Edwin Olofu ya fitar a ranar Laraba 16 ga watan Nuwamba.

Olofu, wanda kuma shine manajan daraktan jarida Platinum Post ya bayyana cewa, wadanda za su halarci zaman za su tafka muhawara ne kan yadda za a yi zabe cikin lumana a badi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, Hamza Al-Mustapha zai yi fashin baki kan maudu’i matsalolin na zamani da kalubalensu da kuma illar hakan ga zaben 2023.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 14 hours 4 minutes 21 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 15 hours 45 minutes 46 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com