Kasar Ghana ta nemi gafarar Najeriya kan yadda aka rusa ofishin Jakadancin ta a kasar, yayin da ta kaddamar da bincike domin gano dailin rusa ginin.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mataimakin ministan harkokin wajen Ghana Charles Owiredu ya bayyana takaici kan rusa ginin, wanda yace hurumin gwamnatin Ghana ce ta kare shi kamar yadda dokar diflomasiya ta tanada.
Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya bayyana matakin a matsayin ta’addanci.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro dauke da makamai suka raka motar da ta rusa sabin ginin a karshen mako, matakin da ya haifar da suka mai karfi daga ciki da wajen Najeriya.












