Dakarun sojojin Nijeriya sun sami nasarar hallaka mayakan ISWAP dake tsaka da karbar horo da IED ta samar a yankin tafkin Chadi.
Wani harin sama da dakarun sojojin saman Nijeriya suka kai kan mayakan kungiyar boko haram tsagin ISWAP yayi sanadiyyar mutuwar mayakan 24.
PRNigeria ta ruwaito cewa atisayen ya faru ne ranar lahadi a Tumbum hamma, guda cikin sananne wurin da mayakan na ISWAP ke karbar hro a yankin Tafkin Chadi.
Read Also:
Wata majiyar liken asiri ta tsaro ta shaidawa PRNigeria cewa ‘yan ta’addan da aka hallaka na gudanar da aikin sarrafa makami da kuma hada bama-bamai wadanda ke karbar horo har tsawon kwanaki shida (6) a jere.
A wani labarin makamancin wannan, PRNigeria ta tattaro cewa wani jirgin yakin sojojin saman Nijeriya (NAF) karkashin rundunar sojin sama ta Operation Hadin kai (OPHK) ya kai wasu hare-hare ta sama kan wata maboyar ‘yan ta’adda a Tumbun da ke kusa da tafkin Chadi.
Wannan wani bangare ne na martani kan mayakan bisa yunkurin sun a kai hari wani sansanin soojin Nijeriya da ke Mallam fatori.
By PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 22 hours 16 minutes 49 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 23 hours 58 minutes 14 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com