RAHOTO NA MUSAMMAN: Al’ummar Maraba Takushara, dake birnin Abuja na fuskantar koma baya duk da cigaban da ake samu a birni

Daga: Kabir Akintayo Fassara: Rabiu Sani Hassan
An bayar da labarai da dama na bincike game da al’ummatai dake kwadayin arziki da cigaba bisa kusancin su da shi, amma a Zahiri abin takaici ne yadda al’ummar ke rayuwa cikin rashin sa’a. wannan shi ke alamta yadda muke rayuwa a Nahiyar Afirka, rayuwa ce cikin albarkatu masu tarin yawa amma mafi yawa cikin halin matsin da komajin talauci.
Kwatankwacin irin wannan ke faruwa da ‘marabar takushara’ wani kauye dake karkashin kwaryar birnin Abuja (Abuja Municipal Area Council) dake yankin Apo Mechanic village.
Kauyen na cikin kwaryar birnin Abuja, birnin dake cike da tarin arziki gami da madudiyar dukiya, sai dai Al’umma kauyen na cikin halin kakanakayi, kuma yana karkashin AMAC guda cikin kananan hukumomi mafiya Arziki a kasar, duk da haka kauyen da Al’umma dake rayuwa a cikin sa na rayuwa tamkar beran masallaci, saboda talauc.
Dagacin garin yace, a kalla kauyen mutane dubu daya (1,000) ke rayuwa a cikin shi,  ba tare da asibiti, Makaranta, wutar lantarki, ko kuma Ruwan sha da amfanin yau da kullum ba, ga kuma matsalar rashin tsaro da suke fama da ita.
Kauyen ya kunshe Al’umma mabiya Addinan Islama da Kirista daga mabambanta kabilu. Amma dai manyan kabilu a garin sun hadar da kabilar Tiv, Gbagyi da kuma Fulani. Noma ce babbar sana’ar su. Yayin da tsarin gine-ginen su yayi kama da dadadden tsari, sabon gini dai kawai shine wani masallacin aka gina.
A shekarar 2019, anyi garkuwa da wasu yara uku dake kan hanyar su ta zuwa makaranta dake kauyen souka. Nisan dake tsakanin kauyen Takushara da Souka kilomita 2 ne.

Shugaban matasan kauyen Vincent Faga, yace yaran sun kwashe makwannin Uku a hannun masu garkuwa da mutane, wadanda daga baya suka sako su bayan gaza iyan biya kudin fansa. Wannan lamari ya dade yana damun Al’ummar yankin, iyayen yaran kuma ya tilasta musu ficewa daga kauyen ba tare da an gano ko ina suka nufa ba.
Tawagar Wakilanmu da suka ziyarci kauyen sun tabbatar da cewa babu wata alamar tsaro ko kuma gwamnati domin ofishin ‘yan sanda mafi kusa da kauyen, na kauyen ‘Waru’ gari mai nisan kilomita 10 da kauyen.
” ’Yan sanda basa sintiri a kauyen mu, suna zuwa ne kawaii dan wani abun tashin hankali ya faru, kuma shima sai an gayyace su. Muna kasada ne da da rayukan mu. Inji wani mazaunin kauyen.
Wani lamari ya taba faruwa a garin a damunar data gabata, yayin da wasu yara suka je dauko ruwa, wasu biyu cikin su suka sulluba cikin ruwa. Al’ummar yankin na fama da matsalar rashin ruwa, mafi akasarin Ruwan da ake amfani dashi a garin ana debo shi ne, kasancewar birtsatsen guda daya ace itama sanata mai wakiltar Birnin Abuja Philip Aduda ne ya samar da ita kuma tana da nisami mita 200 daga kauyen, domin tana cikin kauyen Souka.
Matan maraba takushara sun koka matuka ga tawagar wakilan namu game da halin da suke ciki, a hanyar su ta tafiya kauyen dauke da daron dauko ruwa a kawunan su.
Akwai rijiyoyin burtsatse guda biyu da suka lalace a kauyen, daya dalibai da suka yi hidimar kasa a kauyen suka samar da ita, daya kuma wata kungiya ce mai zaman kanta (NGO) ta samar. Da aka tambaye shi rijiyoyin burtsatsen da aka yi watsi da su, wani mazaunin unguwar, Francis, yace ”Duk wadannan rijiyoyin bas u yi shekara day aba, ‘yan kwangilar sun yi aikin da ba ingantacce ba. Mun yi kokarin mu kula da su, amma ruwa ya daina fitowa daga cikin rijiyoyar. Shi kuwa wanda wata kungiya mai zaman kanta ta samar mana da shim un yi kokarin gyara shi bayan ya lalace amma hakan mu bai cimma ruwa ba.
Baya ga rijiyar burtsatse, akwai kuma rijiyoyi guda biyu da ke tsakiyar garin, guda daya a rufe take, dayar kua dake bude na hade da sabon masallacin da aka gina. Limamin masallacin ya koka kan yadda ake takurawa rijiyar wajen dibar ruwa musamman lokacin rani. Inda yace duk Ruwan zai bushes ai sun shiga kauyukan makota domin samun ruwa.
Mercy, wata matar Aure tace “Gaskiya matsalar mu a wannan kauye shine Ruwan sha, duk da cewa mukan zuwa kududdufi domin debo Ruwan da zamu wanke kayan mu, mu kuma debo wanda zamuyi amfanin gida, amma samun Ruwan sha yana zame mana tamkar yaki, akwai wasu kebabbun lokuta da suke bude mana rijiyar, idan ka rasa wannan lokacin to said ai ka sake bari zuwa washe gari kafin ka sami ruwan da zaka sha”.
Kan batun harkokin lafiya a kauyen kuwa, shugaban al’ummar kauyen, Chief Faga hirinya, na kwance yana jinya tsawon watanni. Dan sa, Francis Faga, yace mahaifin nasa na fama da matsalar barin jiki (Stroke) da ciwon suga (diabetes).
Ya bayyana damuwar su kan yadda suke jigida da mahaifin nasa zuwa cibiyar lafiya ta ‘Waru’ dake kusa dasu.
Faga yace “Mahaifina na fama da lalurar barin jiki (stroke) tsawon watannin 6, da fari mun koma nema masa magani a gida, amma sai muka lura da yadda lafiyarsa ke kara tabarbarewa, shine muka garzaya dashi asibitin Waru nan aka kwantar dashi, anan ne ya gano cewa yana dauke da ciwon sukari, amma an bamu shawarar fara yi masa magani kafin shanyewar barin jiki daya.”
Ya bukaci mahukunta, da sauran daukacin al’ummar Nijeriya da su kawo musu dauki kasancewar yadda aka yi watsi dasu da makomarsu.
Al’ummar basu da asibiti, basu da wuri shan magani, duk da yake dai akwai wani asibiti mai zaman kansa, duk da shima baya wani aiki. Ziyarar da tawagar ta kai ya kara fallasa halin da al’ummar wannan yanki ke ciki, babu kowa cikin asibitin sai wani ma’aikaci guda daya zaune a karkashin wata bishiya. Mista Elisha Godiya wanda shi ne shugaban ma’aiktan jinya, y ace, suna fuskantar kalubale da dama kamar rashin kyawun hanyoyi da ke han su samun magunguna ga marasa lafiya da sauran kalubale da suke fuskanta
Haka kuma dan shugaban Al’ummar kauyen Faga ya bayyana wani labari abin dari, kan wata mata da ta haihu, aka sallame ta ba tare da sanin babban likita ba, alhali tana dauke da ‘yan biyu a cikinta, bayan tahowar ta hanya ta haifi na biyun, wannan ne ya sanya Al’umma suka daina kai kansu wannan asibiti.
Lokacin annobar murar mashako ta Corona (COVID-19) al’ummar sun ce sun rasa mutane biyar sakamakon barkewar cutar.
“Abin ya kure, kawai mutane za su farka su fara amai, mun yi zargin Ruwan rafi ne, kuma rashin kula da lafiya a matakin farko a cikin al’umma ya sa muka rasa rayuka da dama. Kafin mu garzaya da su Waru, yawancin su sun zama gawa” A cewar Faga.
Yace jami’an gwamnati sun sha zuwa kauyen domin gudanar da bincike, bayan sun karbi bayanan ko wanne mutum dake kauyen sai su alkawarta cewa zasu dawo da kayan tallafi, tare da jawo hankalin gwamnati domin tallafa musu kan halin da suke ciki, amma daga bisani said ai kaji shiru babu wanu abu da zai biyo baya.
Godknows Nyamvi dan asalin Maraba Takushara ne, wanda ke da ilimi da gogewa, kasancewar yafi kowa tarin abokaia birni, yayi korafi kan rashin ingancin ilimi da kananan yara ke fuskanta a kauyen.
“tun bayan da lamarin garkuwa da mutane ya faru, iyayen yara da dama suka cire kananan yaran su daga makaranta, suka bar iya wadanda ska data suka cigaba. Idan ana ruwa gadar dake tsakanin takushara da souka ruwa kan shanye ta, kai tsaye dai tana yanked ama shiga kauyen domin zuwa makaranta.
“muna ta karfafa musu gwiwar su kai yaran su makaranta, amma kaso 70 cikin dari basa zuwa makarantar saboda matsalar rashin tsaro” a cewar sa.
Al’ummar sun yanke shawarar gina wani karamin dakin daukar karatu a kauyen, suka kuma bukaci malamai guda biyu wadanda zas uke biya. Yaran dake kasa da shekaru biyar su zauna a kauyen yaran da suka dara haka kuma su tafi makarantar dake Saouka.
Mun tambayi mai Magana da yawun Sanata Aduda, Mista Joseph, kan shin ko sanatan yasan halin da Al’ummar ke ciki, ya ce “Sanatan ya mayar da hankalin sa ne kan ayyukan mazaba da suka rataya a wuyan sa, dukkan wani abu bayan wannan ba aikin sa bane. Aikin sa kawai shine ya gudanar da aiki ya mika shi ga Al’umma. Yadda kuma za’a tafikasa da shi wannan bai shafi sanatan ba. Kuma zai iya yin aikin mazaba ne da majalisar dattawa ta amince da shi. Duk wani abu da ba wannan ba, ba zai iya yin sa ba.
Yana Magana ne kan rijiyar Ruwan dake kauyen souka wanda sanata Aduda ya samar wadda tayi nisa da kauyen Takushara, suke shan wahala kafin su dauki ruwa a cikin ta.
Mun tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sanda birnin Abuja DSP Josephine Adeh kan yanayin tsaron kauyen, inda tace ‘yan sanda na iya bakin kokarin su domin rage yaduwar aikata laifuka a birnin, ta kuma ce an samar da dakarun hadin gwiwa da suka hadar da sojoji da ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro, domin magance ayyukan garkuwa da mutane daga birnin da makotansa.
Ta kuma bayyana cewa daga cikin nasarorin da wannan dakarun hadin gwiwar suka samu har da kama masu garkuwar a Kwali dake yankin kwaryar birnin na Abuja.
Dukkan kokarin da mukarin da mukayi domin jin ta bakin Ministan Birnin na Abuja Hon. Muhammad Bello, kasancewar mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Abubakar Sani bai amsa kiran mu da sakon kar ta kwana da muka tura masa ba.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 13 hours 34 minutes 29 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 15 hours 15 minutes 54 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com