Gwamnatin jihar Kano ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje a shirye ya ke ya sanya hannu kan sammacin kashe malamin Abduljabbar Nasiru Kabara.
Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar, Lawan Musa ne ya bayyana hakan a yayin da yake mayar da martani kan hukuncin da aka yankewa Abduljabbar na hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan da wata kotun shari’ar musulunci ta same shi da laifin yin kalaman batanci ga Annabi S.A.W.
Musa ya ce gwamnan a shirye yake domin ganin ba a karya doka da oda a jihar kano ba, inda ya ce hukuncin da kotun ta yanke akan malamin gwamnatin jihar ta shigar da karar malamin, wanda hakan ke nuna babu wanda ya fi karfin doka.
Read Also:
Ba za a bar kowa ya karya doka ba tare da daukar matakan da suka dace akansa ba.
“Mun kai shi (Abduljabbar) kotu, muka ba shi dukkan abubuwan da ya kamata domin ya kare kansa, kuma a yau mun gode wa Allah, kotu ta gamsu da hujjojin da muka gabatar a kansa, kuma ta yanke masa hukuncin da ya dace,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Kamar yadda gwamna bai canza matsayarsa ba a al’amarin Hanifa, haka nan ma ba ta canza ba akan wannan lamari.
“Kun san akwai tsare-tsare da yawa da ya kamata a bi kuma mai girma Gwamna a shirye yake; da zarar an kawo masa wannan takardar, zai sa hannu domin zartar da hukuncin”. a cewar kwamishinan
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 35 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 17 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com