Ƙasar Amurka za ta bayar da ƙarin tallafin dala miliyan biyar domin taimaka wa yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a faɗin Najeriya.
Read Also:
Tallafin ƙari ne kan dala miliyan ɗaya da hukumar bayar da tallafi ta ƙasar Amurka ta bayar domin taimaka wa waɗanda ambaliya ruwa ta shafa a ƙasar.
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya sauka a daminar bana ya shafi fiye da mutum miliyan 4.4 a faɗin ƙasar, lamarin da ya raba mutane sama da miliyan 2 da muhallansu, tare da lalata dubban gidaje. Inda kuma sama da mutum 660 suka rasa rayukansu.