Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci da ƙaruwar farashin dala na shafar ‘yan Najeriya da wasu ƙasashe masu tasowa.
Rahoton ya ce waɗannan al’amura biyu sun tilasta wa mutane da dama a ƙasashe masu tasowa daina yin wasu muhimman abubuwa, ciki har da rashin samun abin da za su ci, da tilasta wasu cire ‘ya’yansu daga makarantu.
Rahoton wanda aka fitar cikin watan Disamba ya ce farashin abinci ya ƙaru a ko’ina, inda ya kai matakin da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihi, kamar yadda ƙungiyar kula da rikice-rikice ta duniya ta bayyana.
Read Also:
“Wannan barazana ce ga abinci a faɗin duniya, to sai dai matsalar ta fi ta’azzara ga ƙasashe masu tasowa da ke sayen abincin daga ƙasashen waje.
Kuma sabanin matsalar abinci da aka fuskanta a baya, a yanzu ana fuskantar matsaloli biyu ne ciki kuwa har da batun tashin farashin dala wanda da ita ne ake cinikayya tsakanin kasashe”.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa duniya ta fuskanci manyan matsalolin tashin farashin abinci guda uku a wannan ƙarni da muke ciki.
Duniya ta fuskanci tashin farashin abinci na farko a wannan ƙarni tsakanin shekarar 2007 zuwa 2008, sai na biyu tsakanin shekarar 2010 zuwa 2012, sai kuma na yanzu wanda annobar Korona da yaƙin Ukraine suka haddasa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 12 hours 15 minutes 38 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 57 minutes 3 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com