Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar ya kaddamar da wani kwamiti da zai duba tare da yadda za’a samar da wata sabuwar Kwalegin koyar da harkokin kiwon lafiya domin magance matsalolin rashin Likitoci a kano da ma Nigeria baki daya.
Gwamna Ganduje ya kaddamar da kwamitin ne Mai mutane 19 yayin taron majalisar zartarwar ta jiha na wannnan makon wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar kano.
Ganduje ya bukaci yan kwamitin da su zage damtse wajen sauke nauyin da aka dora musu akan lokaci duba da muhimmanci da yadda al’ummar jihar kano ke bukatar Kwalegin saboda karacin jami’an lafiya da ake fama da su.
Ya ce an dorawa kwamitin Alhakin aikin tsara yadda za’a samar daga Kwalegin da inda za’a samar da ita da Kuma tabbatar da tsarin karantarwa a Kwalegin da dai sauransu.
Da yake jawabi bayan mika masa takardar shaidar kama aiki Shugaban kwamitin Farfesa Abdulsalam Nasidi ya ce an samar da kwamitin a lokacin daya dace, idan akai la’akari da yawan al’umma da kuma karancin jami’an kula da lafiya a Kano.
Ya kuma ce bada tabbacin zasu yi aiki kamar yadda ya kamata domin tabbatar da samar da Kwalegin, Inda yace zasu kammala aikin cikin wata guda kamar yadda Gwamnan ya bukata.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 29 minutes 42 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 11 minutes 7 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com