Home General Nijeriya na da kwararrun likitocin Koda 250 kawai

Nijeriya na da kwararrun likitocin Koda 250 kawai

Wani kwararren likitan koda a cibiyar lura da cutar koda ta Zenith dare birnin Abuja a Nijeriya, Dakta de faponle, ya bayyana cewa kasar nada kwararrun likitocin a fannin cutar koda 250.

Faponle ya bayyana hakan ne ranar laraba a birnin Ilorin yayin da yake gabatar da wata Makala a babban taron kimiyya na shekara-shekara da kungiyar likitoci masu neman kwarewa suka shirya a jami’ar Ilorin (ARD-UITH).

Masani yayi magane kan “kariyar koda: yadda cutar ke kara kamari, tare da kira domin daukar mataki.

ya koka bisa karancin kwararru a fannin lalura ta koda a fadin kasar, inda ya kara da cewa  sun yi kadan su iya lura da wadanda ke dauke da cutar a fadin Nijeriya.

Ya bayyana lalura ta koda matsayin cuta ta biyar dake assasa mutuwa a fadin duniya, wadda ke jan ragamar matsalolin lafiya a duniya.

“kaso daya ciki 8 na Al’ummar duniya nada matsalar koda, dukkan namiji daya cikin biyar na dauke da cutar, yayin damace daya cikin 4 ke dauke da cutar,” kamar yadda yace.

Faponle ya bayyana cutar ta koda matsayin cutar dake haba da kadan-kadan, wadda ke dakile koda wajen gudanar da aikinta yadda ya kamata a cikin shekaru da dama abinda ke kai ga lalacewar ta baki daya.

Ya kuma jaddada muhimmancin koda cikin gabban dan adam na yadda take aikin tace guda da abubuwa maras kyau daga cikin dan Adam.

“ana kallon ta matsayin gama mafi amfani a jikin dan Adam, wadda take tace jini har sau Arba’in a rana daya. Babu wata wani mashin da ai iya yin wannan aiki,” a cewar sa.

Ya kara da cewa sun fahimci mutanen dake dauke da cuta ta koda basa fahimtar suna dauke da ita doin alamun fasa bayyana a farko-farkon cutar.

Daga bisani yayi gargadi kan masu yawan ta’ammali da magungunan gargajiya, dasu guji yin hakan, tare da yawaita shawo kan hawan jini da ciwon siga.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp