Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya INEC ta dage gudanar da zaben Gwamnoni dana ‘Yan majalisar Jihohin kasar zuwa 18 ga watan Maris, 2023.
Guda cikin kwamishinonin hukumar ne ya sanar da Jaridar Punch daukar matakin duk da bai bayyana dalilin daukar matakin ba.
Read Also:
Tun da fari dai hukumar ta sanya ranar 11 ga watan Maris matsayin ranar da zata gudanar da zaben, sai dai kuma wannan sanarwa ta tabbatar da karin mako guda kafin gudanar da shi.
Tun da fari dai Shugaban hukumar zaben da Kwamishinoninsa sun shiga wata ganawar sirri kan zaben Gwamnoni da na ‘yan Majalisar dokokin da misalin karfe 7 na daren Laraba.
PRNigeri Hausa