Kungiyar lauyoyin Nijeriya ta NBA ta umarci gwamnatin tarayyar kasar da ta gaggauta bin umarnin kotun kolin kasar na kara wa’adin karbar tsoffin kudin data sauyawa fasali.
Shugaban kungiyar na kasa Yakubu Maikyau ne ya bayyana hakan ta cikin wata samara da ya fitar ranar litinin a kasar.
Wannan na zuwa ne tun bayan da kotun kolin kasar a ranar 3 ga watan maris ta bayar da umarnin a cigaba da karbar tsoffin kudin har zuwa 31 ga watan disambar 2023.
Read Also:
Tun bayan da kotun kolin da bayar da umarnin gwamantin tarayya kasar da babban bankin kasar na CBN basu fitar da sanarwa ga al’ummar kasar domin cigaba da amfani da tsofaffin takardun kudin ba.
Shugaban kungiyar lauyoyin ta NBA ya nuna matukar damuwar sa kan yadda sauyin kudin ya jefa al’ummar kasar cikin halin kakanakayi, inda yace yin watsi da hukuncin kotu da gwamantin tarayya kasar tayi ya nuna zagawar kundin tsarin mulkin kasar tare da damukradiyya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 17 hours 47 minutes 57 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 29 minutes 22 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com