Gwamnatin Najeriya ta sanar da jinkirta lokacin gudanar da Shirin kidayar jama’ar kasar da aka shirya yi a wannan wata na Maris zuwa watan Mayu mai zuwa.
Ministan yada labarai Lai Mohammed ya sanar da haka bayan wani taron majalisar ministoci a fadar shugaban kasa da aka gudanar ranar laraba.
Mohammed ya danganta dage shirin da jinkirta zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da hukumar zabe tayi, abinda ya jirkita shirin hukumar kidayar.
Read Also:
Ministan yace majalisar ministocin Najeriya ta amince da bukatar hukumar na karbar kudin da ya kai naira biliyan 2 da miliyan 800 domin sayen na’urorin zamanin da za’ayi amfani da su wajen gudanar da aikin.
Rahotanni sun ce za’a gudanar da kidayar ce daga ranakun 3 zuwa 7 ga watan Mayu kamar yadda aka baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara.
Kidayar jama’a na daya daga cikin ayyuka masu sarkakiya a Najeriya saboda banbance banbancen dake tsakanin al’umma wadanda ake zargi da aringizon jama’a duk lokacin gudanar da irin wannan kidayar. Rabon Najeriya da gudanar da kidayar jama’a tun daga shekarar 2006.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 20 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 1 minute 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com