Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta tabbatawar wa ‘yan Nijeriya dake neman aiki a hukumar cewa ta shawo kan matsalar da ake fuskanta a shafinta na daukar aiki da nufin ganin an sami mafita daga yanzu zuwa ko wanne lokaci.
Read Also:
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran hukumar Femi babafemi ya fitar, mai dauke da kwanan wata 15 ga watan Maris 2023. Inda yace sa’oi kadan da bude shafin a ranar lahadi 12 ga wata Maris, ya fara samun tangarda sakamakon yadda mutane sama da dubu 200 ke kokarin cike takardar samun gurbin aiki a hukumar.
Domin warware wannan matsalar hukumar a ranar talata 14 ga watan Maris ta inganta shafin domin daukar dimbin masu bukatar samun gurbin aiki a hakumar bayan da sama da mutane 53,170 suka nasara shiga tashin.
A halin yanzu, shafin yana aiki yadda ya kamata. Don haka hukumar na amfani da wannan dama wajen neman afuwar wadanda suka bibiyi shafin bisa tsaikon da suka samu da su kara hakuri.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 hours 8 minutes 39 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 50 minutes 4 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com