Wata gobara ta tashi a kasuwar gamboru da ke tsakiyar birnin Maiduguri a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotonni sun ce gobarar ta ta shi ne da tsakar ranar Asabar lokacin da ake tsaka da kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi da ake gudanarwa a faɗin ƙasar.
Read Also:
Kawo yanzu babu rahotonni rasa rai sakamakon wannan gobara da ta tashi a kasuwar ta kayan abinci a jihar.
Kawo yanzu dai ba a kai ga sanin takamaimen abin da ya ya haifar da gobarar ba.
idan ba a manta ba makonni uku da suka gabata wata gobara da ta tashi a kasuwar Monday market a birnin na maiduguri inda ta yi sanadiyyar asarar miliyoyin dukiyoyi.
PRNigeria Hausa