Zulum yayi nasara da kuri’u sama 545

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya sake samun nasarar komawa wa’adi na biyu na mulkin jihar, bayan nasarar da ya samu a zaɓen gwamna da aka gudanar a ransar Asabar ɗin da ta gabata.

INEC ce ta bayyana ɗan takara a matsayin wanda ya lashe zaɓen a Maiduguri babban birnin jihar a ranar Litinin.

Zulum ya lashe zaɓen ne da ƙuri’a 545,542 sai kuma jam’iyyar PDP ta ke da ƙuri’u 82,147.

Jam’iyyar LP wadda ta taka rawar gani a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabirairu ta zo ta uku da kuri’a 1,517.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com