Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi a Arewa mask gabashin Najeriya ta shirya muƙabala tsakanin malamai da kuma Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi kan kalaman da ya yi game da Annabi Muhammadu (SAW).
Wata wasiƙa da hukumar ta aike wa malamin, ɗan asalin jihar Bauchi, ta ce za a gudanar da tattaunawar ilimin ne gobe Asabar, 8 ga watan Afrilu a birnin Bauchi.
A farkon makon nan ne kalaman malamin suka fara tayar da hazo musamman a shafukan zumunta, bayan ya yi iƙirarin cewa “ba ya buƙatar taimakon Annabi”.
“Ana gayyatar ka zuwa tattaunawa ta ilimi [munaƙasha] game da kalamanka cewa ‘kai! …Manzon Allah ma ba ma son taimakonsa, ƙarewarta kenan’,” kamar yadda hukumar ta bayyana cikin wasiƙar.
Read Also:
An ga malamin ya bayyana cikin wani bidiyo a ranar Alhamis yana cewa ya ji daga wata majiya cewa zai yi muhawara da wakilan wasu ƙungiyoyin addini a jihar, waɗanda suka haɗa da Izala da ɗariƙa.
An yi irin wannan muhawara a Kano cikin watan Yulin 2021 lokacin da aka zargi Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da yin kalaman ɓatanci ga Annabin Muhammadu.
Bayan muhawarar ne kuma, hukumomi suka gurfanar da malamin a gaban kotu, wadda ta yanke masa hukuncin kisa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 3 hours 13 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 4 hours 55 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com