Rahotanni daga Nijeriya na bayyana cewa Mutane 214 ne suka mutu tsakanin watan Janairu da Maris din shekarar 2023, a hare-haren ‘yan bindiga da rikicin ƙabilanci da hare-haren ɗaukar fansa a jihar Kaduna a Najeriya.
A cikin wannan adadi 14 mata ne a yayin da huɗu yara ne ‘yan ƙasa da shekaru 18.
A gundumar Kaduna ta Tsakiya, an samu rahoton mutuwar mutane 115 (kashi 54 bisa dari na yawan adadin).
Ɗari da takwas na waɗannan adadi sun faru ne a yankunan ƙananan hukumomin Birnin Gwari, da Giwa, da Igabi, Chikun da kuma Kajuru.
Read Also:
Ƙananan hukumomi Giwa da Birnin Gwari duka sun samu yawan adadin mutane 32 da suka mutu, karamar hukumar Chikun 25, Igabi 13, sai Kajuru shida a watannin ukun farkon shekarar 2023.
A yankin kudancin Kaduna an samu mutuwar mutane 61 a daidai irin wannan lokaci.
Yanayin kai hare-hare da na daukar fansa, da munanan tashe-tashen hankula na addini da na kabilanci – tsakanin hare-haren ‘yan bindiga – sun faru a karamar hukumar Zangon Kataf, inda mutane 19 suka rasa rayukansu.
Mutane 12 ne kuma aka kashe a ƙaramar hukumar Sanga a cikin watanni ukun farko na shekarar 2023.
Yankin arewacin jihar ya shaida mutuwar mutane 38 a watanni ukun farko, inda aka samu mutuwar mutane 22 a karamar hukumar Zaria.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 41 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 22 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com