Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yayi alkawarin ragewa ‘yan Najeriya radadin cire tallafin man fetur ta hanyar bunkasa bangarorin sufuri, da ababen more rayuwa, da ilimi, da samar da dawwamammen hasken wuta lantarki, da kuma inganta bangaren lafiya.
Shugaba Tinubu yayi wannan alwashi ne lokacin dayake jawabi ga ‘yan Najeriya akan zagayowar ranar dimokradiyya.
Read Also:
Mista Tinubu yacigaba da cewa, ” A ranar demokradiiya ta wannan shekara, Ina kira garemu da mukara sadaukar da kanmu domin karfafa wannan tsari na gwamnati daya baiwa kowa ‘yancinsa, wanda hakan kuma shine tsarinmu tsawon wadannan shekaru 24 da dawowar mulkin demokradiiya.”
A ranar 29 ga watan mayu lokacin dayake jawabi bayan amsar rantsuwa, Shugaba Tinubu yabayyana cire tallafin mai kacokan lamarin daya saka al’ummar kasar cikin rudani biyo bayan tashin gouron zabi da farashin mai da sauran kayan masarufi sukayi a fadin kasar.
Shugaba Tinubu yayi allawarin tabbatar da bai baiwa ‘yan Najeriya kunya ba, tahanyar cika alkawurran daya dauka lokacin yakin neman zabe.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 18 hours 8 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 49 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com