Matasa a jihar kano na cigaba da yin tir gami da ala-wadai da ayyukan sabuwar gwamnatin jihar kano na rusau.
Abduljalil AbdulRahman na guda cikin matasan ‘yan kasuwa dake kallon muddin sabuwar gwamnatin bata sauya fasalin yadda take tafikas da mulkin jihar ba, hakan ka iya sauyawa jihar suna daga “tumbin giwa zuwa tumbin akuya”
“jihar kano ta ginu ne ta fuskar kasuwanci, itace cibiyar kasuwancin da babu kamar ta a nahiyar Afirka, wannan rushe-rushe ka iya haifar da nakasu, yasa jihar ta tashi daga tumbin giwa domin kasaitar ta tumbin Akuya.
“kano, ta yi shuhura, shekaru aru-aru a fannin kasuwanci, banga dalilin da zai saka don wani yayi kuskure a lokacin gudanar da mulkin sa ba kaima a matsayin na shugaba kazo kan gudanar da abinda kai tsaye zamu iya kiran shi da kuskure”
“Ko ba komai dai ya kamata a bawa mutanen nan lokaci a kalla wata daya domin su kwashe kayan su, idan ya so a ‘yan tsakanin sai sus an mene abin yi”
“amma yanzu anzo ana rushe musu wurin neman abinci inda suka dogara dashi kuma babu wani tanadi nan ema musu mafita, a haka ake tunanin za’a cigaba da kiran jihar da tumbin giwa”
Daga bisa ya bayyana cewa wannan mataki bazai haifarwa da gwamnatin jihar kano da Al’umma jihar da mai ido ba.
Read Also:
Tun bayan karbar rantsuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamna Jihar Kano ya fara aiwatar da abubuwan da ya alkawarta wa Kanawa, musamman kan gine-ginen da gwamnatin jihar karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta gina.
Domin nuna wa Kanawa da gaske gwamnatin da yake jagoranta karkashin inuwar jam’iyyar NNPP take tun bayan rantsar da shi, gwamnan ya fara dirar mikiya a filin sukuwa da ke unguwar Nasarawa, inda Gwamna Abba ya kaddamar da rushe wasu rukunin kantuna guda 90 da ake zargin na dan Gwamna Ganduje ne.
Daga nan ne kuma ya dira a tsohon otal din Daula, bisa zargin Ganduje da yin watandar filin.
harabar masaukin alhazai ta gamu da sabon matakin gwamnatin, inda nan ma aka tabbatar da tarwatsa wuraren da aka rabar wa wasu masu kwalli a ido kamar yadda sabuwar gwamnatin ta ce.
Haka zalika tawagar rusau ta sauka a filin Idi, inda aka fara ruguje kantinan da ke cikin filin idin kafin wayewar gari aikin gama ya gama.
Tun dai bayan daukar wannan mataki na gwamnan jihar kano, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya shawarci Gwamnatin Abba kan cewa ba haka ya kamata ta yi ba, domin kamata ya yi a samar da wani ingantaccen kwamiti ko neman shawarar masana kan yadda ya kamata a fuskanci ire-iren wadannan wurare da ake zargin an raba su ba bisa ka’ida ba.
Ya ce, “Gaggawa aikin shaidan ne, saboda haka akwai bukatar nutsuwa, sannan a yi kokarin duba maslahar al’umma ba yin fushi da fushin wasu ba.”
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 7 minutes 53 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 49 minutes 18 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com