Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta baiwa ofishin sakataren gwamnatin jihar umarni daya fara aiwatar da shirye shiryen tantance ‘yan asalin kano domin daukar nauyin karo karatu a kasashen waje.
Read Also:
Acikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnatin tace wannan dorawa ne akan Shirin da gwamnatin kano karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tayi a shekarar 2015 na daukar nauyin daliban Kano masu digiri mai daraja ta farko 503 domin cigaba da karatunsu a kasashe akalla 14.
Sanarwar ta Kara da cewa ” la’akari da wannan mataki, ana gayyatar duk wadanda suka dace dasu aike da takardunsu domin karo karatu a shekarar karatu ta 2023/2024.
Duk wanda yake son morar wannan tsari dole yakasance dan asalin kano Kuma Wanda keda digiri mai daraja ta daya (First class) ko mai kama dashi, sannan yakasance mai lafiya.”
Sanarwar ta cigaba da cewa, duk wadanda suka cika ka’idojin sai su aike da takardunsu ta adireshin yanar gizo www.kanostategov.ng. kafin daga bisani a gayyacesu domin tantancewa.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 54 minutes 56 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 36 minutes 21 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com