Manyan ƙungiyoyin ƙwadago biyu a Najeriya za su gana da jami’an gwamnati don kokarin ganin sun amince da sabon mafi karancin albashi da kuma wasu bukatu na ma’aikata bayan da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur.
Ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Najeriya ta ce yau ne wa’adin da ta ba gwamnatin tarayya ke cika, kan bukatarta mayar da mafi karanci albashi naira dubu 200 sakamakon janye tallafin mai.
Ƙungiyar ta ce bukatar biyan mafi kakantar albashin naira dubu 200 na cikin bukatun da ta mika wa gwamnatin Tarayya, domin ragewa ma’aikata raɗaɗin wahalar janye tallafin mai da sabuwar gwamnatin ta yi.
Read Also:
sakatare janarar da kungiyar Comrade Nuhu Toro, ya bayyana wa manema labarai cewa suna kan bakansu akan albashi mafi ƙanƙanta na naira dubu 200 ga ƙaramin ma’aikaci a Najeriya domin tsadar rayuwar da mutane suka shiga.
Ya ce “Farashin kayayyaki da rayuwa ma gaba daya tsada ya keyi, saboda haka gwamnati ba ta da hujja illa ta ƙarawa ma’aikata mafi ƙanƙantar albashi na naira dubu 200 domin su ma’aikata su suke ƙirƙirowa ta arzikin ƙasa”.
“Gwamnati za ta iya biyan wannan albashin idan ta rage almubazaranci, idan ta rage sama da faɗi da dukiyan talakawa, kuma idan ta rage kashe kuɗi a kan abubuwan da bai kamata ba.”
Toro ya dai ƙara da cewa dole ne gwamnati ta rage yawan kashe kudin da take yi, shi ne za ta sami yanda za tayi ta biya ma’aikata albashi mafi ƙanƙanta naira dubu 200.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 5 minutes 2 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 46 minutes 27 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com