Babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya ce babban abin da ya fi dacewa da ƙasar a wannan zamani shi ne mulkin dimokradiyya.
Babban hafsan sojin ya bayyana haka ne a lokacin bikin yaye manyan sojoji da aka gudanar da makarantar yaye manyan hafsoshi ta Jaji da ke Kaduna, kamar yadda wata sanarwa da kakakin rundunar Burgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar.
Laftanar Janar Lagbaja ya ce dole ne a tunasar da sojojin ƙasar cewa taimakonsu wajen tabbatuwa da ɗorewar mulki shi ne babbar hanyar nuna ƙwarewa a aikin soji.
Ya kuma ce babban burin kowanne ɗan Najeriya a yanzu shi ne ɗorewar mulkin dimokradiyya, wanda zai tabbatar da haɗin kan ƙasa da kuma kare muradun ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambanci addini ko na ƙabila ba.
Read Also:
”A don haka ina kira ga duka sojojin Najeriya su bayar da gudunmowarsu wajen tabbatar da ɗorewar mulkin dimokraɗiyya, sannan su kauce wa shiga lamuran siyasa a lokacin gudanar da ayyukansu”, in babban hafsan sojojin.
Ya kuma jaddada burin rundunar sojin ƙasar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ƙasar.
Laftanar Janar Lagbaja ya ce sojojin ƙasar tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaron ƙasar na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da kare martabar ƙasar.
Babban hafsan sojin na wannan jawabi ne a daidai lokacin da ƙasashen ƙungiyar Ecowas suka bai wa sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum a Nijar wa’adin mako guda na su mayar da shi kan mulki su fuskanci tarin takunkumai, ciki har da na matakin Soji.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 3 hours 49 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 5 hours 30 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com