Home Labarai Gwamnatin tarayya Nijeriya ta kafa kwamitin kan harkar tara haraji

Gwamnatin tarayya Nijeriya ta kafa kwamitin kan harkar tara haraji

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da wani kwamiti da zai yi garambawul a harkar tara haraji da manufofin kuɗi, a yunƙurinsa na ganin haraji ya zama kashi 18% na arziƙin da Najeriya ke samu cikin duk abin da ta sarrafa a gida, wato GDP, nan da shekara uku.

Shugaban ya ce matakin zai taimaka wajen ganin Najeriya ta rage dogaro a kan bashi wajen samun kuɗin gudanar da harkokin gwamnati.

Wata sanarwa da mashawarcin shugaban Najeriyar na musamman kan harkar yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar ta ambato Tinubu na umartar shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele, ya yi nazari don gyaran fuska a harkokin kuɗi da garambawul a harkar tara haraji da kuma kyautata bunƙasar tattalin arziƙi a cikin shekara ɗaya.

Tinubu ya ce Najeriya har yanzu tana fuskantar ƙalubale a ɓangarorin da suka haɗar da biyan haraji cikin sauƙi, kuma kason haraji da take karɓa idan an kwatanta da kuɗin da take samu daga duk abin da ta sarrafa a gida ya yi kaɗan. A cewarsa ƙasar, ta zama kurar baya a Afirka a wannan ɓangare.

Sanarwar ta ce manufar shugaban ƙasar ita ce yi wa tsarin karɓar haraji gyaran fuska don tallafa wa bunƙasa harkokin ci gaba mai ɗorewa.

Ya ce matuƙar babu kuɗin shiga, gwamnati ba za ta iya samar isassun ayyukan inganta rayuwa ga al’ummar da suka ba ta amana ba.

Shugaba Tinubu ya ba da umarnin cewa ana sa ran kwamitin zai gabatar da wani tsarin garambawul cikin gaggawa da za a iya aiwatarwa a cikin kwana 30. Sai kuma ba da shawarwari kan muhimman sauye-sauye a cikin wata shida, aiwatar da cikakkun tsare-tsaren a cikin shekara ɗaya.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Darakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da Wiwi
X whatsapp