Kotun sauraron ƙorafin zaɓe da ke zama a Kano ta soke zaɓen Honourable Muktar Umar Yarima mai wakiltar Tarauni a majalisar wakilai saboda amfani da takardu shaidar kammala karatu na bogi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A hukuncin da alƙalan kotun uku suka bayar, sun ce sun samu Yarima da gabatar da takardar kammala karatun firamare na bogi, don haka kotun ta umarci hukumar zabe ta ƙasa ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Honourable Hafizu Ibrahim Kawu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
A baya dai jami’in sanar da sakamakon zaben mazabar Tarauni, a zaɓen da ya gabata, Garba Galadanci ya sanar da Yarima na jam’iyyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan samun ƙuri’a 26,273, ya kuma doke Honourable Hafizu Ibrahim Kawu na jam’iyyar APC wanda ya samu ƙuri’a 15,931.
Daga baya Kawu ya shigar da ƙara, inda ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen a bisa zargin gabatar da takardun bogi daga ɓangaren wanda ya yi nasarar.












