Nasarorin da malaman musulunci suka cimma bayan tattaunawa da shugabannin mulkin soji na Nijar

Tun da aka fara wannan hayaniyar ta juyin mulkin Nijar babu wata tawaga da ta cimma manufarta kuma cikin tattaunawa da kuma lalama kamar yadda malamai suka cimma.

Daga bayanan da na tattara daga yammacin jiya zuwa yau abin sai son barka.

1- Firaministan da sojoji suka naɗa da ministocin mulkin soji ne suka tari tawagar malaman musulunci da suka je Nijar bisa sahalewar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, don shiga tsakani.

2- Kai tsaye aka wuce da tawagar malaman musulunci zuwa fadar shugaban kasa.

3- Malaman Najeriya sun tattauna sosai da Firaminista da kuma wasu daga ministoci kan yadda za’a samu masalaha da kyautata alakar Nijar da Najeriya.

4- Tawagar malaman ta share kusan Awanni 3 tana tattaunawa da shugaban mulkin soji na Nijar.

5- Shugaban mulkin soji ya amince cewar bisa jagorancin malaman zai bude kofar tattaunawar difilomasiyya don samun matsaya.

6- Shugaban mulkin soji na Nijar ya bada sakon hakuri zuwa ga gwamnatin Najeriya, kan kin amsar bakuncin sarkin Musulmi da tsohon shugaban kasa Abdussalami Abubakar da ECOWAS ta aike a matsayin manzanni na musamman.

Yace barazanar tsaro da aka fuskanta bayan Najeriya ta katse wutar lantarki da kuma fargabar abinda ka’iya faruwa da su in akaji labarin sun shiga Nijar dai dai lokacin da aka datse kaiwa kasar abinci da wutar lantarki ya sanya suka ki amsar bakuncinsu.

Zamu Iya cewa su dai malaman musulunci sun sauke nauyi, kuma sun yi Iya nasu.

Abinda ya rage yanzu shine, wadannan nasarori da malamai suka samu zasu tabbata ne Idan ECOWAS ta rungumi hanyar tattaunawa, sannan gwamnatin Najeriya ta tsagaita da daukar matakai da zasu jefa alummar Nijar cikin garari da kuma firgici da matsin rayuwa.

Allah ya sakawa malamanmu da Alkhairi, wutar da ake son kunnawa tsakanin Najeriya da Nijar malamai sun kamo bakin zaren yazuwa yanzu.

Dukda ana ganin matakan da ya dauka sunyi tsauri a farko, amma dole ka jinjinawa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ya amince malamai su shiga tsakani.

A bayanan da na samu, tawagar malaman da suka je Nijar, gwamanti ce ta shige gaba wurin ganin sun ziyarci jamhuriyar Nijar, kuma an hadasu da shugaban kamfanin mai na kasa NNPCL da darakta a fadar shugaban kasa.

Karibullah Abdulhamid Namadobi
[email protected]
Kano State

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 18 minutes 42 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 7 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com