Wata kungiyar matasan Arewa maso Gabas Youth Progressive Union da Coalition for Democratic Rights Group sun bukaci gwamnonin Arewa da su yi koyi da salon kawar da fatara da kuma bunkasa rayuwar bil’adama da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar kano ya ke yi wanda suka bayyana a matsayin wanda zai taimaka wajen cigaban jihar.
Kungiyoyin matasan arewa maso gabas sun yi wannan kiran ne a ranar Laraba a Yola, babban birnin jihar Adamawa, a wata ganawa da suka yi da manema labarai.
Idan zaku iya dai zaku iya tunawa a makon daya gabata, gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta sake farfado da tsarin ilimi ga talakawa wanda tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fara, wadda ta samar da damammaki na ilimi kyauta, guraben karatu na gida da waje ga dalibai sama da 1,001 da aka zabo a sassan jihar, matasan dai dukkanin su sun karatunsu na digirinsu na farko, Inda gwamnatin ta turasu domin yin digiri na biyu.
Kwamitin Gwamnatin Kano na tantance ma’aikatan da Ganduje ya dauka aiki ya mika rahotansa
Da yake jawabi, Shugaban kungiyar North East Progressive Union Dokta Kabir Hassan Sambo, ya bayyana damuwarsa kan bambance-bambancen da ake samu a fannin ilimi a tsakanin yankin Arewa da Kudancin kasar Nigeria, inda ya yi kira da a gaggauta yin koyi da manufar inganta Ilimi ta Kano a yankin da ke fuskantar kalubale daban-daban na tattalin arziki.
Read Also:
Dokta Sambo ya ce: “Abin da ya kamata a sani shi ne, a cikin watanni 5 da suka gabata Gwamna Yusuf ya biya kudin koyarwa, ciyarwa da kuma masaukin dalibai 1001 Post Graduate zuwa Indiya. Ya kuma biya wa dalibai 57,000 kudin jarrabawar Sakandare (NECO), da kudin koyarwa na dalibai 7,000 a Jami’ar Bayero, haka kuma daliban manyan makarantu a Kano an yi musu rangwame kashi 50 cikin 100 na kudadensu. Bugu da kari, ya sake bude cibiyoyi 26 na koyon sana’o’i domin inganta rayuwar mazauna jihar Kano.
“Muna bukatar dukkan gwamnonin Arewa da su yi koyi da wadannan matakai da gwamnatin Kano ta dauka, su kuma ba da fifiko ga ilimi da Gina dan adam.”
Da suke karin haske kan mahimmancin siyasa da tattalin arzikin Kano ga sauran sassan Arewa, matasan Arewa maso Gabas sun ce, “muna sane da cewa Kotun sauraren kararrakin zaben ta kori wannan mutumi da ya sabunta kwarin gwiwar matasa a Arewacin Najeriya. Kamar yadda matasa a Kano suke, matasan Arewa sun zuba ido a kan yadda ake shirin yanke hukunci a Kotun daukaka kara. Dole ne a sami Adalci. Adalci shi ne ginshikin dimokuradiyya, idan har tsarin shari’a ya gaza wa jama’a, to dimokuradiyya tana cikin hadari!”
Bugu da kari, matasan sun bayyana cewa, “Ba mu manta da irin rawar da jihar Kano ta taka a matsayin cibiyar kasuwanci da harkokin siyasar Arewacin Najeriya a da da yanzu ba, don haka ya zama wajibi ‘yan siyasar arewa su yi koyi da jihar kano don cigaban al’ummar yankin .”
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 50 minutes 23 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 31 minutes 48 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com