Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA ta ce za ta bi kadin abinda wasu bata-gari suka yi wa jami’anta a karshen makon da ya gabata
Shugaban Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka ta cikin wata takardar manema labarai da kakakin hukumar Nabilusi Abubakar Na’isa ya fitar mai dauke da kwanan watan 31/10.2023 aka kuma raba ga manema labarai a jihar Kano.
Read Also:
Yayin da yake duba biyu daga cikin jami’an hukumar da ke kwance a asibitin Murtala da asibitin Kashi na Dala, Shugaban ya ce, ba zai zuba ido ya bari ana cin zarafin jami’an ba, a don haka ya bayar da tabbacin mika lamarin wajen jami’an ‘Yan Sanda domin fadada bincike tare da daukar matakin da ya kamata.
Haka Kuma, Tawagar shugaban Hukumar ta kai ziyarar Ta’aziyya ga jami’inta mai suna Nasiru Sani Abubakar a unguwar Yakasai Wanda Allah ya yi wa rasuwa sakamakon bige shi da mota ta yi; Ya yi Ta’aziyya ga iyalan jami’in tare da adduar samun gafara a gare shi da sauran alumma gaba daya.
Daga bias ya ja hankalin jami’an Hukumar da su ci gaba da gudanar da aikin su cikin kwarewa da mutunta jama’a.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 12 minutes 39 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 15 hours 54 minutes 4 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com