Tinubu ya bukaci majalisar wakilai ta amincewa da kasafin tiriliyan 2.1

Hoton Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya rubutawa majalisar wajilan Nijeriya wasika kan su amince da kwarya-kwaryar kasafin kudi na naira tiriliyan 2.1 domin kara albashin ma’aikata da kuma wasu sabgogi tsaro da sauransu.

Haka kuma shugaban ya aikewa majalisar da tsarin kasha matsakaici na tsakanin shekarar 2024-2026 zuwa ga majalisar.

A ranar litinin, majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da Karin kasafin kudin shekarar 2023 na  naira tiriliyan 2.1.

Yayin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan fitowa daga taron  majalisar ta tattalin arzikin a Abuja, ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, yace an amince da kasafin ne domin magance wasu lamurran kudi na gaggawa

Ministan ya bayyana cewa “Majalisar ta amince da kwarya-kwaryar kasafin da aka bukata matsayin kasha na biyu a shekarar 2023,”.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 6 minutes 33 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 10 hours 47 minutes 58 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com