Kungiyar kwadago ta kasa ta zargi rundunar ‘yansanda ta kasa da lakadawa shugabanta na kasa Joe Ajaero duka, bayan sun yi awon gaba dashi a tsakar ranar jiya a jihar Imo.
Shugaban yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar, Benson Upah shine ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren laraba, lokacin da yake tabbatar das akin shugaban nasu, bayan ya wuni a hannun jami’an yansanda.
Jami’an yansanda sunce sun tsare shugaban kungiyar kwadagon ta kasa ne domin bashi kariya bayan ya fuskanci cin zarafi.
Read Also:
Sai dai jim kadan da sakin shugaban kungiyar kwadagon ta kasa kwamared Joe Ajaero ya tabbatar da cewar an lakada masa duka sannan aka yi awon gaba dashi zuwa wani wuri da bai sani, wanda a nan ne aka gallaza masa.A wani labarin kuma Hukumar Kula Da Yanayi Tayi Hasashen Samun Hazo Da Kura A ‘Yan Kwanaki Masu Zuwa
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 17 hours 48 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 30 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com