Mukaddashin shugaban hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya bukaci hukumomin jin dadin Alhazai na jihohin Nijeriya da su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun rage kudin hajjin shekarar 2024.
ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da yake karbar bakuncin sakatarori da shuwagabannin, da kuma shuwagabannin sojojin Nijeriya a shalkwatar hukumar dake birnin tarayya Abuja.
Read Also:
haka kuma ya bukaci su dasu sanya kudin da suka karba zuwa yanzu a asusun hukumar ta NAHCON, domin adadin kudin su zasu bayyana mataki na gaba da za’a dauka.
“babu lokaci, ya kamata ku sanya kudin da kuka karba a Asusun NAHCON, domin yin shirye 0 shiryen farko kafin aikin Hajjin, gami da ziyara domin kulla alaka da ayyukan da za’a gudanar a yayin aikin hajjin.
“ta yadda mutanen mu zasu gansu da kokarin mu da nasarorin da zamu samu sakamakon shirin da mukayi don aikin hajjin shekarar 2024 ya zo cikin sauki,” a cewar sa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1240 days 4 hours 41 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1222 days 6 hours 23 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com