Mai Bincike CBN ya gayyaci Shugaban bankin Titan Trust

Mai Binciken Musamman kan badakalar Babban Bankin Najeriya, CBN, Jim Obazee, ya gayyaci Shugaban bankin Titan Trust Bank, Tunde Lemo da wasu mutum biyu masu hannayen jari a bankin, “domin wata ganawa” dangane da abin da ke tattare da sayen hannayen jarin kadarorin Bankin Union a shekarar 2022.

Ta cikin wata wasika da mai Bincike ya aika wa Tunde Lemo, sa’o’i kaɗan bayan ya fito ya ƙaryata zargin da ake yi masu.

Tunde dai tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya ne, kuma ana zargin rawar da ya taka wajen cinikin.

Cikin rahoton da Obazee ya damƙa wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, a ranar 20 Ga Disamba, ya bayyana cewa Lemo a lokacin da ya ke Mataimakin Gwamna ga Godwin Emefiele a CBN, ya yi amfani da maƙudan “kuɗaɗe ta hanyar haram” ta kafa bankin Titan Trust Bank, sannan ya yi amfani da kuɗaɗen ya saye Bankin Union da Keystone Bank, ta hanyar amfani da sunayen wasu ‘yan kamasho.

Obazee ya rubuta a cikin rahoton sa cewa Gwamnatin Tarayya ta gaggauta ƙwace TTB daga hannun Tunde, domin ya kafa bankin da kuɗaɗen da ya sata a CBN.

A martanin sa, Tunde Lemo ya yi bayani a ranar Lahadi cewa bankin sa ya bi ƙa’ida bai bauɗe ko kaɗan ba.

Cikin watan Oktoba ne SSS suka yi cacukui da A’isha, Mataimakiyar Gwamnan CBN, dangane da zargin karkatar da Dala Miliyan 300 zuwa Bankin Titan da Polaris.

Hukumar Tsaro ta SSS sun damƙe Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, A’isha Ahmed.

An kama ta ne dangane da hannun da ta ke da shi wajen yadda aka bi bauɗaɗɗiyar hanyar danƙara hannayen jari a bankunan Polaris Bank da Titan Bank, wato Union Bank na da.

Aisha Ahmad ita ce Mataimakiyar Gwamnan CBN mai lura da yawan kuɗaɗen hada-hada a bankuna.

Wani rahoto da gidan Talbijin din kasar na NTA ya bayyana cewa, ta na da hannu wajen yadda aka dauki Dala miliyan 300 a boye don sayen hannayen jari da bankin Polaris da bankin Titan, wato Union Bank a dai sauran su.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 20 minutes 11 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 1 minute 36 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com