Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aza harsashin ginin gada mai hawa uku da zata lashe Naira biliyan 27 a mahadar Dan’agundi, da kuma Tal’udu duk a cikin birnin Kano.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin tofa ya fitar kuma aka raba manema labarai a jihar.
Read Also:
A yayin a aza harsashin ginin, gwamnan ya ce an fara gudanar da manyan ayyukan ne domin rage cunkoson ababen hawa, da saukaka zirga-zirga, da kawata birnin, da hana gurbatar muhalli, da samar da ababen more rayuwa ga al’umma.
Haka Kuma gwamnan ya nanata alkawuran gwamnatinsa na samar da ababen more rayuwa a jihar tare da kudurin samar da karin ribar dimokuradiyya musamman ga wadanda aka zalunta.
Ya ce matsayin jihar na babban birni ta cancanci a samar da gagarumin sauyi na ababen more rayuwa domin biyan bukatun mazauna birnin sama da miliyan goma da inganta zamantakewa da tattalin arzikin mazauna birnin.
PRNigeria hausa