Tsohon mataimakin shugaban Kasar Najeriya Atiku Abubakar ya ce dole ne gwamnati mai ci ta ɓullo da hanyar magance wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki a wannan lokaci.
Atiku ya bayyana haka ne a sakonsa na barka da sabuwar shekara ga ƴan Kasar. inda ya ce dole gwamnati ta nuna wa ƴan ƙasa alkibla ko kuma inda manufofinta suka dosa ba wai barinsu a cikin duhu ba.
“Da gwamnati ta yi dabara wajen tsara manufofinta da ba mu shiga irin wannan kangi da muke ciki ba. Iyalai da kuma masana’antu da yawa na cikin wane hali a yanzu,” in ji Atiku.
Read Also:
Ya ce ya zama tilas a tashi domin fuskantar batun hauhawar farashin kayayyaki, taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma rashin tsaro a sabuwar shekara da nufin magance su.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce shekara ta 2023 na cike da kalubale masu tarin yawa, sai dai ya kamata a ɗauki darasi domin fuskantar gaba.
“Idan muna son fita daga wannan kunci da muke ciki, dole ne mu yi tunani mai kyau da kuma samar da tsare-tsare na ƙasa waɗanda za su sa talakawan Najeriya su zama ginshikin ci gaban mu,” in ji Atiku.
Wazirin na Adamawa ya taya dukkan ƴan Najeriya murnar sabuwar shekara tare da yin kira ga kowa da ya tashi haikan don ganin iyalai da sana’o’in sun kasance cikin yanayi mai kyau.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 23 hours 5 minutes 5 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1222 days 46 minutes 30 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com