Dakarun sojin saman Nijeriya sun sami nasarar hallaka jagoran mayakan ISWAP Ba’a Shuwa a jihar Borno.
Harin na ranar talata yayi sanadiyar mutuwar mayakan na ISWAP da dama sun.
Zagazola Makama mai bincike kan lamurran da suka shafi tsaro a yankin tafkin Chadi, ya ruwaito cewa harin da yayi sanadiyar Shuwa ya auku ne a Kwatan Dilla, dake karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.
Read Also:
Yace hotuna sun nuna yadda gawarwakin mayakan da aka hallaka ke kwance.
Mayakan dai na boye a wata maboyar su domin gujewa luguden wuta da sojojin ke yi a yankin Timbuktu triangle.
Shuwa ya zama jagoran ISWAP a shekarar 2021, bayan mutuwar Abubakar Shekau.
Haka Kuma ya jagoranci gudanar da ayyukan ta’addanci Chiralia, Markas Kauwa, Abirma, Buk, Abulam, Dusula, Abbagajiri, Gorgore da sauran yankuna da dama na Timbuktu da Alagarno a jihar Borno.
Shuwa da tawagar sa na da alhakin hare-haren bama bamai a garuruwan Damaturu-Maiduguri, Askira, Buratai, Buni Yadi, Buni Gari, Gaidam da sauran yankunan dake jihohin Borno da Yobe.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 19 hours 40 minutes 40 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 21 hours 22 minutes 5 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com