Gwamnan jihar Sokoto yace zai dauki mataki kan rahoton cin bashi

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu ya musanta bayanan da ke ƙunshe a cikin rahoton hukumar kula da basussuka ta Najeriya dake cewa gwamnatinsa ta ƙarɓi bashin kimanin naira biliyan 89 a cikin gida da kuma kusan dala miliyan talatin da bakwai daga waje.

Gwamnan ya ce bai ci bashin ko sisin kwabo ba a cikin watanni goman da ya yi yana gwamna, “Ko tsakanin mutum da mutum za a ƙarbi bashi akwai yarjejeniya balle bashin da ya shafi gwamnati, kuma ana bin dokar zuwa majalisa kafin a anso bashin amman mu ba mu yi ko wanne ba.”

Alhaji Ahmed Aliyu ya ce rahoton ƙarya ne bai da asali bai da tasiri, kuma yana kira ga dukkan wanda ya ce ya ci bashi ya zo ya bada shaidar hakan,” Idan ma an yi domin a ɓata mani suna ne, hakan bai shiga ba saboda a matsayina na gwamnan jihar Sokoto tun lokacin da na anshi mulki ina biyan albashi 18 ko 19 ko 20 ga wata.”

Gwamnan ya bayyana cewa ba wai yana nufin ba zai ci bashi a nan gaba ba, amman dai a halin da ake ciki bai ci bashi ba, kuma babu wani dan kwangila da ke binsu bashi.

Alhaji Ahmed Aliyu ya shaida cewa zai dauki mataki kan rahoton da aka yi masa ƙazafi. “Abin da muke samu da shi muke amfani muna yin abubuwan da suka kamata.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 18 hours 2 minutes 19 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 43 minutes 44 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com