Babbar kotu da ke jihar Legas ta bayar da umarnin ci gaba da tsare tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
Za a ci gaba da tsare Emefiele a hannun hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa har zuwa ranar 11 ga watan Afrilu da kotu za ta yanke hukunci kan ba shi beli.
Tun farko da ya bayyana a kotun, tsohon gwamnan babban bankin Najeriyar ya musanta sabbin tuhume-tuhumen da ake masa na karya dokokin da suka shafi hada-hadar kuɗaɗen waje da hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arzikin ƙasa take masa.
EFCC ta zargi Emefiele da ware wasu kuɗaɗen waje kusan dala biliyan biyu ba tare da bin ka’ida ba.
Wannan na cikin tuhume-tuhume 26 da ake masa a ƙarar da aka gabatar gaban babbar kotun.
Matakin ya ƙara ta’azzara taƙaddamar shari’a tsakanin EFCC da tsohon gwamnan babban bankin wanda kuma yake fuskantar tuhuma kan almundahana da rashawa da haɗa baki wajen aikata laifi a Abuja, babban birnin Najeriya.
Read Also:
Emefiele, wanda ya bayyana gaban babbar kotu a Legas karƙashin mai shari’a Rahman Oshodi, ya musanta aikata zarge-zargen da ake masa.
An karanto masa tuhume-tuhume 26 da ake masa da wanda ake kararsu tare Henry Omoile.
Dukkansu sun musanta zarge-zargen da ake masu, Sun kuma nemi kotu ta bayar da su beli zuwa lokacin da za a saurari ƙara.
Lauyan Emefiele, Lebi Lawal ya ce ya kamata kotu ta duba matsayin wanda yake karewa.
A cewar lauyan, “tsawon shekara tara, Emefiele ne ma’aikacin banki na ɗaya a Najeriya.
Lauyan ya kuma roƙi kotu ta sake nazari kan ɗabi’un Emefiele tun bayan kama shi.
Bayan hawansa kan mulki ne, shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele daga shugabancin babban bankin ƙasar.
Makonni bayan dakatar da shi ne kuma aka kama shi tare da gurfanar da shi gaban shari’a a watan Nuwamba kan zarge-zargen almundahana.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 11 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 15 hours 52 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com