Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sake yin sabbin nade-nade a cikin kunshin gwamnatin jihar.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Sanarwar ta ayyana Farfesa Ibrahim Magaji barde matsayin mai bada shawara na musamman ga mai girma gwamna fannin harajin cikin gida.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
- Dr. Abdulhamid Danladi, mai bawa Gwamnan shawara kan ‘yan kano mazauna ketare na II
- Engr. Bello Muhammad Kiru, Mai bada shawara na musamman fannin Albarkatun ruwa.
- Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye) da aka sake nadawa matsayin Mai bada shawara na Musamman kan matasa da wasannan.
- Sai kuma Dr. Nura Jafar Shanono da aka matsar daga matsayin Mai bada shawara na musamman a fannin Albarkatun ruwan, zuwa babban managan hukumar (WRECA).
- haka kuma sanarwa ta bayyana daga likkafar Hon. Baba Abubakar Umar daga mai bada shawara na musamman zuwa babban sakataren hukumar dake lura da makarantu masu zaman kansu na jihar kano.
- An kuma nada Hon. Nasir Mansur Muhammad a matsayin babban daraktan dake lura da kanana da matsakaitan sana’oi (SMEs)
- Aminu Hamidu Bako Kofar Na’isa zai zama mataimakin babbana daraktan (DMD), a ma’aikatar aikin gona da cigaban karkara ta (KNARDA).
haka kuma an nada Engr. Mukhtar Yusuf, matsayin mataimakin babban daraktan (DMD) a hukumar (WRECA).
Daga bisani sanarwar ta tabbatar da cewa nadin ya fara aiki nan take, tare da fatan kammalawa lafiya da nasara.
PRNigeria Hausa












