Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ayyana ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu, 2024 matsayin Kari cikin ranakun hutu a kasar, a wani bangare na bukukuwan karamar sallah ta shekarar 1445 bayan hijra.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakatariyar ma’aikatar cikin gida Dr. Aishetu Gogo Ndayako.
Read Also:
Sanarwar ta ambaci ministan ma’aikatar Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, na taya daukacin Al’ummar Musulmin kasar murnar kamala ibadar azumin watan Ramadan cikin kwanciyar hankali, inda kuma ya bayyana kudirin shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu na samawa ‘yan kasar kyakkyawan yanayi.
Idan zamu iya tunawa jaridar PRNigeria ta ambaci ministan ya ayyana ranar talata 9 da kuma 10 ga watan Afrilun, 2024 matsayin ranakun hutun karamar a kasar.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 34 minutes 0 second,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 15 minutes 25 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com