Kotu ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga APC

Wata babbar kotu a jihar Kano ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Idan dai za’a iya tunawa kwanaki biyu da suka gabata ne shugabancin APC na mazabar Ganduje a Karamar Hukumar Dawakin Tofa, mahaifar Ganduje, ya dakatar da shi bisa zargin cin-hanci da rashawa da gwamnatin Kano ke yi masa.

Ta cikin umarnin kotun, ƙarƙashin Mai Shari’a Usman Na’abba, ta hana Ganduje, wanda shine tsohon gwamnan Kano, nuna kan sa a matsayin shugaban jam’iyyar APC.

Na’abba ya kuma hana Ganduje yin wani taro ko daukar mataki a matsayin shugaban jam’iyyar har sai an kammala zaman sauraron karar.

Ya kuma hana shugabancin jam’iyyar na jiha shiga cikin maganar da take gaban kotu.

Dr. Ibrahim Sa’ad, a madadin biyu daga cikin shugabannin APC na mazabar Ganduje, mataimakin sakatare, Laminu Sani da mai baiwa jam’iyyar shawara kan harkokin Shari’a, Haladu Gwanjo ne ya shigar da karar.

Haka kuma kotun ta umarci waɗanda ake kara su hudu da suka haɗa da jam’iyar APC a matakin kasa da jiha da kuma shi Ganduje din da su tsaya a matsayin su daga 15 ga Afrilu zuwa 30 ga watan Afrilu lokacin da za a saurari karar.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 29 minutes 43 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 11 minutes 8 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com