PDP ta yi kakkausar Suka kan Batun Karin Albashi a Nijeriya

Babbar jam’iyyar hamayya a Nijeriya PDP, ta yi kakkausar suka ga gwamnatin kasar bisa jagorancin jam’iyyar APC, game da karin albashin da gwamnatin ta yi, da cewa wani mataki ne na an yi ba a yi ba.

Domin kuwa jam’iyyar PDPn na ganin an yi karin albashin ne yayin da jama’ar Najeriya ke ta fama da matukar tsadar man fetur da tsadar kayan abinci da dai sauran matsalolin da suka haifar da tsadar rayuwa.
Ta cikin wata ganawa da yayii da manema labarai, Ibrahim Abdullahi, mukaddashin jami’in hulda da jama’a na jam’iyar na kasa ya ce, halin da Najeriya ta shiga a ƙarƙashin mulkin APC cikin shekaru tara, ya sanya ƴan ƙasar sun koma mabarata saboda yunwa “Ana fuskantar mummunan rashin tsaro da halin ha’ula’i da ƙasa ta shiga.”

Ibrahim Abdullahi, ya ce abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta samar da tsaro ga manoma domin su noma abincin da ƙasa za ta samu ya wadata domin a samu sauƙin abincin.

A ranar Talata, kwana ɗaya kafin ranar bikin ma’aikata ta duniya ne ofishin kula da albashin ma’aikata a kasar ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa an yi wa ma’aikatan gwamnatin tarayya ƙarin albashi da kashi 25 zuwa 35 cikin ɗari.

Lamarin ya haifar da cece-ku-ce ganin cewa akwai wani kwamiti da gwamnatin ta kafa wanda aka ɗora wa alhakin samun matsaya kan albashi mafi ƙaranci a ƙasar.

Jam’iyyar ta PDP na ganin ko da an yi ƙarin albashi, adadin ƙarin ba zai samar da maslaha ba a cikin halin ƙunci da karayar tattalin arziƙi da suke ciki ba.

PRNigeria Hausa

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 24 minutes 50 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 6 minutes 15 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com