Gwamnatin Najeriya ta musanta iƙirarin da kamfanin hada-hadar kuɗi ta intanet, Binance ya yi kan cewa wani jami’in gwamnatin ƙasar ya nemi cin hanci daga jami’in kamfanin na kuɗin kirifto dala miliyan 150.
Ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ministan yaɗa labari na Najeriya hannun Rabi’u Ibrahim, ta ce zargin na kamfanin Binance wani yunƙuri ne na “ɓata wa Najeriya suna domin ɓoye ayyukan da yake yi na saɓa ƙa’ida”.
Read Also:
Sanarwar ta ce “babu ko ƙwayar zarra ta gaskiya a zargin da kamfanin na Binance ya yi.”
A ranar Talata ne shugaban kamfanin na Binance, Richard Teng ya yi zargin, wanda aka wallafa a jaridar New York Times ta Amurka da ma wasu jaridun duniya a ci gaba da taƙaddamar da ake yi tsakanin kamfanin na kuɗin kirifto da Najeriya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa gaskiyar lamarin shi ne ana ci gaba da tuhumar Binance a Najeriya saboda barin da ya yi aka yi amfani da shafinsa wajen “halasta kuɗaɗen haram da taimaka wa ayyukan ta’addanci da kuma ƙayyade farashin kuɗin ƙasashen ƙetare ba bisa ƙa’ida ba”.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 31 minutes 48 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 13 minutes 13 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com