Ana cigaba da kai ruwa rana tsakanin NLC da Gwamnatin Nijeriya

Gamayyar kungiyoyin kwadago na Najeriya sun sake yin fatali da tayin mafi ƙarancin albashi na naira 54,000 da gwamnatin ƙasar ta amince za ta biya.

A tataunawar da ƙungiyar ta yi da kwamitin ƙarin albashi da gwamnatin Najeriya ta kafa, kwamitin ya yi tayin biyan naira 54,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan kasar.

Hakan kari ne a kan naira 48,000 da kwamitin gwamnatin tarayyar ya yi tayin biya a zaman da ɓangarorin biyu suka yi cikin makon da ya gabata.

NLC ta ce ta yi watsi da tayin ne sakamakon halin matsin rayuwa da ake fuskanta a Nijeriyar.

Bangarorin biyu za su sake zama a rana  Laraba domin ci gaba da tattaunawar kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar.

Tun da farko dai NLC ta ce tana so gwamnatin ƙasar ta biya naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, la’akari da halin da ake ciki  na ƙaruwar hauhawar farashi da karyewar darajar kudin ƙasar.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 21 minutes 25 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 2 minutes 50 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com