An wayi gari da yakin aikin kungiyoyin kwadago a Nijeriya abin da ake tsammanin Akwai yiyuwar ayyukan tattalin arziki a kasar su tsaya cik sanadin yajin aikin.
Kokarin da shuwagabannin Majalisar dokokin kasar suka yi domin sasanta bangarorin ya ci-tura.
Bayan ganawar sa’o’i hudu da shugabannin Majalisar dokokin kasar da yammacin ranar Lahadi a Abuja, shugabannin kungiyar kwadagon sun ce babu gudu babu ja da baya game da yajin aikin gama gari da aka shirya ya fara ranar Litinin 3 ga watan Yuni, 2024.
Sai dai shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ya ce za su tunbi sauran reshoshinsu a kan kiran da shugabannin Majalisar suka yi mu su ma a kan su janye yajin aikin.
Read Also:
“A yanzu ba mu da hurumin janye yajin aikin, yajin aikin zai fara ne yayin da mu mika rokon da shugabbanin Majalisar dokokin kasar suka yi ga rassan mu daban-daban, game da kiran da suka yi a kan mu janye yajin aikin” inji shi.
Tun da farko, Osifo, shugaban kungiyar kwadago (TUC); da takwaransa na kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero; sun gana da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas. a Abuja.
Kungiyoyin kwadagon sun kira yajin aikin ne sakamakon rashin cimma matsaya a tattaunwar da bangarorin biyu ke yi da gwamnatin kasar kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata.
Kungiyoyin kwadago fiye da 10 sun yi kira ga ma’aikatansu da su amsa kiran uwar kungiyar kwadago ta kasa har sai abinda hali ya yi.
Ma’aikatan lafiya da bankunan kasuwanci da na sufurin jiragen sama da na sauran fanonin na cikin wadanda za su shiga yajin aiki, abinda ake ganin zai kawo nakasu ga tattalin arzikin kasar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 17 hours 47 minutes 0 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 28 minutes 25 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com