Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana umarnin ta na bijerewa umarnin gwamnan jihar na fidda tsohon sarkin kano Aminu Ado Bayero daga Gidan sarki na Nassarawa.
Idan za’a iya tunawa a ranar Alhamis gwamnan jihar Kano ta bakin kwamishinan Shari’a na jihar Haruna Dederi ya bawa kwamishinan ‘yan sandan jihar Usaini Gumel kan ya fidda tsohon sarkin daga gidan bisa hukuncin kotu tarayya dake jihar kano da ya tabbatar da dokar da majalisar jihar kano ta samar a 2024.
Read Also:
Da ya ke ganawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch a ranar Juma’a, kwamishinan ‘yan sandan yace bin umarnin gwamnan na fitar da tsohon sarkin tamkar riga malam masallaci ne.
Yace gwamnatin dai da ta bayar da umarnin itace ta shigar da kara gaba gaban babbar kotun jiha akan batun na fitar da sarkin wanda ktoun zata zauna a ranar litinin 24 Yuni 2024.
Tun bayan umarnin gwamantin jihar ta Kano, aka wayi gari da sake girke jami’an ‘yan sanda a harabar gidan sarkin na Nassarawa, inda tsohon sarkin kano Aminu Ado Bayero yace Gwamnatin jihar na tsrae da shi a ciki.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 40 minutes 36 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 22 minutes 1 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com