Gwamnatin jihar Kaduna ta ce jami’an tsaron haɗin gwiwa sun kashe wani jagoran ‘yan fashin daji mai suna Alhaji Kachalla Ragas tare da wasu abokan harkarsa da dama.
Wata sanarwa da Kwamashinan Tsaron jihar Samuel Aruwan ya fitar a yau Juma’a ta ce dakarun rundunar Operation Whirl Punch ne suka yi nasarar kashe shi bayan hare-haren da suka kai ta sama a ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar ta arewa maso yammacin Najeriya.
“Hare-haren ta sama da ƙasa sun yi nasarar kashe ‘yanbindiga da yawa tare da shugabanninsu a dajin Yadi da ke yankin Bula,” in ji sanarwar.
Ya ƙara da cewa an kai harin ne bayan samun bayanan sirri cewa ‘yanbindigar “za su yi wani taro don kitsa mummunan aiki, inda daga baya masu leƙen asiri suka hangi gungun mutum bakwai zuwa 10 ɗauke da makamai”.
“Cikin waɗanda aka kashe har da Alhaji Kachalla Ragas, wanda abokin Buharin Yadi ne wanda shi ma aka kashe kwanan nan,” a cewar sanarwar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 10 hours 13 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 54 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com