Gwamnatin jihar Kano ta zargi rundunar ‘yan Sandan jihar da daukar bangaranci a rikincin Masarautar dake faruwa a jihar.
Daraktan yada labaran Gwamnan jihar Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan ta cikin wata hira da tashar Talabijin ta Channels a cikin shirin Politics Today na ranar Juma’a.
Read Also:
Idan za’a iya tunawa tun bayan da majalisar jihar kano ta yiwa dokar masarautar jihar gyaran fuska, gwamnan jihar ya umarci kwamishinan ‘yan sandan daya fidda tsohon sarki Aminu Ado bayero daga fadar sarkin ta gidan Rumfa.
Sai dai rundunar ‘yan sandan bisa jagoranci CP Usaini Gumel tayi fatali da umarnin gwamnan inda tace umarnin kotu yafi dacewa ta bi.
Ta cikin ganawar Sunusi Bature ya bayyana cewa hukuncin Kotun tarayya su ya bawa nasara domin kuwa kotun bata rushe dokar data sauke tsoffin sarakunan jihar guda biyar ba.
Daga bisani Dawakin Tofa ya bayyana muhimmancin dawo da martabar sarautar kano da ya zargi tsohuwar Gwamnatin Ganduje da kassarawa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 9 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 50 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com