Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a Najeriya ta sake dage sauraren karar da ke neman a tsige tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasar har zuwa ranar 5 ga watan Yuli.
Mai shari’a Inyang Ekwo, a ranar Laraba, ya dage ci gaba da zama sauraron karar a karo na biyu domin baiwa mai kara damar amsa sabuwar bukatar da Ganduje ya shigar na kalubalantar cancantar karar.
Read Also:
A zaman na Laraba, lauyan mai kara, Benjamin Davou, ya shaida wa kotun cewa Sanusi Musa, SAN, wanda ke kare Ganduje, ya mika masa wata sabuwar bukata.
Ya ce zai bukaci lokaci don yin nazari kan ko zai amsa takardar. Lauya Musa bai yi adawa da bukatar Davou na dage zaman ba.
A saboda haka mai shari’a Ekwo ya dage ci gaba da sauraron karar har sai ranar 5 ga watan Yuni domin ci gaba.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 27 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 17 hours 8 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com