Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi gwamnatin kasar ta koma amfani da fasahar zamani a yanƙin da take yi da mayakan Boko Haram da ‘yan bindiga da sauran masu ɗauke da bindiga.
Hakan na ƙunshe cikin ƙudurin da Sanata Ali Ndume ya gabatar don ɗaukar matakin gaggawa kan harin da aka kai a yankin Gwoza da yake wakilta.
Bayan doguwar muhawara da aka kwashe sa’o’i ana yi tare da jajantawa kan harin, majalisar ta yarda cewa amfani da fasahar zamani a yaƙin zai kawo ƙarshen masu kai hare-haren ƙunar baƙin wake.
Haka kuma Majalisar ta amince a ƙara bayar da muhimmanci a yankin tafkin Chadi da dajin Sambisa da Kuma hayin dutsen Mandara.
Da yake bayar da tasa gudunmuwar, Sanata Adam Oshimole ya ce bai kamata a ƙara wa sojoji kuɗi ba da zimmar samar da makaman zamani da kuma fasaha, yana cewa an ba su kuɗaɗen da suke isassu a wannan lokaci.
Sai dai majalisar ta ƙi amincewa da bukatar tasa, inda mafi yawan mambobinta suka yi watsi da buƙatar.
Kazalika wasu daga cikin sanatocin sun nemi gwamnatin Najeriya ta haɗa hannu da kamfanonin tsaro masu zaman kansu domin ci gaba da yaƙi a yankunan Tafkin Chadi da dajin Sambisa da sauran wasu yankuna da ke fama da matsalar tsaro a Najeriya.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 30 minutes 11 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 11 minutes 36 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com