Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA reshen jihar Kano ta bukaci wajabta yin gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi kafin aure a jihar.
Kwamandan hukumar Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Alhamis.
“A yunkurin hukumar na dakile dabiar ta’ammali da miyagun kwayoyi ta gabatar da wannan gwaji don kawar da dabiar daga Nijeriya,” a cewar sa.
Read Also:
Idris Ahmad yace gwajin zai zama wani mataki na magance shan miyagun kwayoyin da kuma kare wadanda basu fara ba daga cikin ma’auratan gami da wayar da kai da fadakar da su hadarin fadawa harkokin shaye – shayen.
Ya ce samar da dokar zai taimaka matuka wajen magance yawan mutuwar aure, gami da rage yawan matan aure dake shiga harkokin shaye – shayen a jihar.
daga bisani kwamandan hukumar ya bukaci wata da matasa da su guji dabi’ar shaye – shaye tare da bata hadin kai don kawar da ta’adar daga jihar da kasa baki daya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 25 minutes 46 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 7 minutes 11 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com